audio
audioduration (s)
1.14k
1.4k
label
class label
0 classes
text
stringclasses
3 values
null
Lungu ne mai dauke da komatsen duwatsu, robobi, leda da kuma fasassun kwalabe, kana ketare wadannan zaka yi karo da katuwar bola mai dankaren wari, musamman a lokacin irin wannan wato damuna. Gefe da bolar daga hannun dama wani kwarmatsattsen gidan kasane mai 'yar guntuwar katanga yana dauke da daki daya tak! sai makewayin langa-langa, daga bayan dakin. Tsakar gidan murhun kasane da 'yar randar ruwa, sai igiyar shanya data raba gidan biyu. Daga nesa kana hango gwangwanayen alwala a jikin langa-langar makewayin. Karamin gadon kara ne a dakin, mai dauke da katifar Rimi, sai jikunan kaya na gana (Ghana must go). Daga bakin kofar akwai 'yar kujerar katako ta zama, kasa kuma an shimfida tabarma. Gida ne na mabukata wanda rashi yayi wa katutu. Na yi saurin maida kwallar da ke zubo min, tare da kara gyara fuskata. Mahaifina Allah ya karbi rayuwarsa tun muna kanana kwarai, danginsa kuma sun yi fatali da al'amuran mu, nice babba sai kannena biyu Aisha da Sumayya. Allah ya jarrabi mahaifiyar mu da ciwon asthma, shi yasa duk talaucin mu baka ganin kura a gidan mu, musamman kura. Karatuna ya tsaya tun shekara biyu da suka wuce, wato lokacin da na gama aji uku. Da farko na fara talla sai muka ga cewa, hakan ba zai fisshe mu ba, shi ne wani aminin mahaifinmu ya samo min aiki a gidan sarauta a matsayin baiwa cikin bayin da aka dauka sabbi. Insha Allahu kuma gobe nake sa ran farawa. Karfe tara. na dare muna shan garin rogo da kuli a matsayin abincin darenmu kamar kullum, Inna ta kalle ni tare da fadin. "Abinda nake son ce miki shi ne, ki yi addu'a Allah ya tabbatar miki da alherin wnn aiki, sannan ya kawar miki da sharrinsa kamar yadda na dage da tawa addu'a ba dare ba rana. Kuma a duk inda kika shiga ki sanya tsoron Allah a zuciyarki, ki tuna matsayin ki dana iyayenki, banda daukar abinda ba a baki ba, wlh ki guji abin hannun mutane ki zauna lafiya. Ban yafe miki ba matukar ba a baki abu ba kika dauka, ko kika roka. Aiki ya kai ki, shi za ki maida hankali ki yi, banda yawan surutun banza idan ba tambayar ki aka yi ba, domin yawan magana na haddasa karya. kada ki manta ko ke wace ce, lokacin da kike cikin gidan sarauta, to ki ringa hango yanayin gidanku. Yi na yi bari ya rabaki da kowa, wlh duk wulakancin mutum duk izgilancinsa, matukar zai ce ka yi ko ka bari kuma ka aikata hakan, to lallai sai dai wani abu, amma ka wuce wulakancinsa. Da fatan kin ji abinda na fada miki?" Na daga kaina Ina fadin, "Insha Allah Inna zan kiyaye". Tayi murmushi, "Allah ya yi miki albarka, je ki sha ruwa ki zo ki kwanta kada gobe ki makara. Na ji shi Mal. Barau yace karfe bakwaiake son ganinku a fada." Na mike Ina fadin, "ko shidane Inna Insha Allahu akan lokaci zamu je". Ta yi 'yar dariya, "ja'ira na sanki da sammako, amma ai dole ki zo ki kwanta din." Washegari a Gidan Sarauta Muka bi layi ana bamu kayan sawa, wanda zamu ringa amfani da su a cikin gidan a matsayin "uniform". Yadi ne mai dan karen kyau, ga taushi ruwan sararin samaniya (sky blue) dinkin riga da siket mai kyau iri daya kuma kowacce za a bata dai-dai ita, kowa kala bibiyu ya samu har aka yi saura, don mu ishirin da shida ne sabbin dauka amma duka babu wanda ta haura shekara ishirin da biyu. Mafi akasari sauran iyayensu a nan suke aiki gidan sarauta, sai mu uku ne kawai wanda muka shigo ta hanyar alfarmma! Abin mamaki har 'yan kunne da sarkar wuya da ta kafa tare da awarwaronsu aka rarraba mana, irin kalar kayan, amman na duwatsu mai haske. Musamman wani fankacecen daki aka bamu domin shiga, wai mu sanya kayan da aka bamu yanzu. Duk wannan bidirin a wani bangare muke cikin gidan ba mu isa inda ake son mu isan ba har yanzu. "Allahumma arzukuna" kawai nake nanatawa lokacin da nake zura kayan a jikina, duk na rude sai kyarma nake yi. Mutum kusan shidasuka hada baki wajen fadamin cewa, NA YI KYAU!! Ni kaina nasan kayan dole su yi min kyau, saboda kalar ita ce wanda na fi so cikin kaloli, ba don komai ba sai don kyan da kalar ke yiwa fatar jikina dake lokacin da ta rabu da ni. Muka biyo layi, dogarai sun saka mu a tsakiya wasu gaba, wasu gefenmu, wasu kuma a bayanmu. Inda duk muka wuce bayi ne ke kara-kaina mana da mata, haka na dinga raba ido Ina kallon aljannar duniya a wannan masarauta, wuce wannan tsuntsu, ruwa, filawowi babu abinda ba mu gani ba har Allah ya Kai mu wani katafaren muhalli. A nan ne naga abin mamaki, mata ce kyakkyawa kishingide bisa wani hadadden gado, bayi kusan goma sha biyu kewaye da ita, wasu na firfita, wasu matsar kafa, wasu na ba ta labari mai dadi don 'NISHADI' banda wanda ke bakin kofa da tsakar dakin suna kara-kaina. Aka gabatar da mu cikin wani irin yanayi na girmamawa duk ina lura da yadda suke yi. Ta kalle mu cikin dan murmushi kadan, ta ce. "karasa da su wurin GIMBIYAR " Nan da nan al'amarin ya daina bani mamaki da fargaba gami da tsoro. Wani bangare muka nufa, sashen da ya firgitani fiye da cikin inda muka shiga, naji tamkar ba a duniya nake ba. Can ma wasu bayin ne bila adadin suna bauta. Mun fi mintuna ishirina tsaye ba tare da wani ya kula da mu ba, dogarawan na tsaye su ma kamar gani suka ba ni tausayi (neman halak da wuya). Zuwa can muka hango 'yanmata biyu da 'yan kwanduna a hannun cake da filawoyi masu kyau ga kamshi suna zubdawa a kasa. Mamakina ya karu ganin wasu nayin shara, wasu na ba tawa. Ai ban karasa mamakin ba na hango hadaddiyar budurwa ta biyo sawun filawoyin ta sha kaya irin na alfarma, ga wata hadaddiyar alkyabba tana faman jan kasa, kanta cikin hular alkyabbar wanda bazar kwaliyar ta boye rabin fuskarta, amma kana iya hango kyallin zinaren da ke falauniya a wuyanta da kunnenta. Har ta zauna saman wata rantsattsiyar kujera ba a bar zubda filawar nan ba. "GIMBIYA!!" Na maimaita sunan ta a cikin raina, Ina kara yi mata kallo. Kusun mintuna goma sha biyarda zamanta amma ko kallon inda muke ba ta yi ba. Tuni kuguna ya soma rikewa saboda ni kam Allah ya sani ba ni da jimirin tsayuwa. Kafin na kai ga sarewa Allah ya taimakeni ta dago kai a hankali kamar mai fama da ciwon sankarau, ta wurgawa dogarawan nan wani mugun kallo, nan da nan naga suna durkusawa suna godiya tare da ficewa da sauri. Ta kalle mu, tare da fadin. "Ku zauna". Nan da nan muka cika umarni. "Kafin na raba muku aiki zan barku anan ku taimakawa sauran domin ku ga yadda ake ya cikin kwana uku, daga safe zuwa karfe shidana marece. Jidda!" Ta kwada kira a hankali. Da gudu ta karaso dattijuwa ta yi kusan kanwa ta hudu da ita, ko kallonta ba ta yi ba, ta ce. "A kaisu ciki suna bukatar horo na kwana ukukafin a raba musu aiki". Ta rusuna tare da fadin. "An gama Gimbiya. Ku taso ku biyo ni". Da sauri muka bita riii... "Inna mutane na wahala a duniyar nan, kuma mutane na jin dadi. Na ga mulki ni HUMAIRA inna, don ba zance ba, ba zan zuba ido ba, ba zan yi wasa ba, zan dage, na samo dan abin dogaro domin share hawayen iyayena. Allah ka taimake ni ka kuma taimaki dukkan masu dogara da kai". Ba ta lura da ni ba. Inna ta ce: "Lallai Allah ba zai bar bawan sa da gaske ba". Inna mutane na wahala a duniyar nan, kuma mutane na jin dadi. Na ga mulki ni HUMAIRA inna, a zage ka, a ci maka mutunci sannan kayi godiya. Kai SARAUTA wata aba ce! Wallahi inna kwana biyu nan ba ki ji yadda jikina ke yi min ciwo ba. Tayi murmushi tace, "Dama ai sai a hankali zaki saba kuma ai gobe ne kawai ya rage da an raba muku aikin bashi ke nan ba. Tunda kince akwai na safe akwai kuma na rana dana dare kinga idan na safe Allah yaci da ke, karfe bakwaikina can biyukin dawo gida idan na rana ne kuma biyukina can shidakin dawo idan kuwa na dare ne bakwaiidan kika tafi sai safe bashi ke nan ba? Ke dai ki sanya tsoran Allah a duk inda kike ki kuma tuna yana ganinki a kowanne hali kika sami kanki. Aikin nan mai wahala ne mutuka domin shi ba wani share-share ko goge-goge ke gajiyar da bayi a gidan sarauta ba, a'a, cin fuska da izgilanci ke ba kowa wahala don haka sai an daure. Mai nema yana tare da samu. Ki tuna idan baki daure kika hakura ba, ina zamu samu abincin da zamu ci? Ruwan sha har gagararmu yake yi a gidan nan sai mu roko a makota. Ga karatun 'yan uwanki tun da ke baki samu halin yiba sannan uwa uba aurenki idan ya tashi wa zai bamu? Daga dangina har na mahaifinki kin dai san yadda ake. Saboda haka kiyi hakuri wata rana sai labari." Na yi murmushi kawai domin a ganina kamar na fi Inna sanin wadannan abubuwan. Kamar kullum muka isa gidan cikin lokaci ni da Amira wacce muke tafiya tare kwana biyu sakamakon gidansu na bayan namu babu nisa kuma nice ke biya mata safiya idan muka dawo zata rako ni har kofar gida kafin ta koma nasu. Muna cikin wankin gimbiya misalin karfe goma sha biyu na rana ina ta al'ajabin wai har da wandunanta da rigunan nono shin ita bata jin kunya mata bada wadannan wurin wanki. Na wani haukan nake ganin kamar wani sirrinta ne wanda ya kamata ace ita ke kula da abinta. Kai wani abin sai gidan sarauta. "HUMAIRA!" Na yi saurin waigawa, "Na'am." "Bar musu wankin kizo gimbiya na son ganinku." Ina kyarma na dauraye hannaye na cikin gudu-gudu sauri-sauri na karasa saboda na lura latti na saurin hasala gimbiya. Duk abinda ta umarta lallai tana son ayi mata shi da sauri cikin gaggawa. Na iske su Amira a layi kamar ranar farko. Ni mana bi sahu ta yatsina fuska tana kallonmu daya bayan daya kamar mai kallon tsohon ciwo a jikin kazamin mutum. "Ku kasu gida uku," ta fada a wahale. Cikin 'yan mintuna da basu wuce biyu ba muka rabu kamar hanya. Abin haushi Amira bata kusa dani don haka ya kasance bata cikin namu gungun ma'ana nasu daban. Ta nuna su Amira da baki daga yau zaku shiga cikin 'yan aikin rana. Gabana ya fadi nan da nan na hau addu'ar zuci kada Allah ya hadani da aikin dare saboda Inna. Bana tunanin zan iya barinta ta ringa kwana ita kadai sai su Sumayya saboda cikin dare asmarta na iya tashi. Ta juyo garemu. "Cikinku, kulululu kune masu aikin safe. Wadannan kuma su shiga cikin masu kwana." A hankali na furta Alhamdulillah. "Saboda haka ku na dare kuna iya tafiya sai shida kwazo tare da yan kwana na safe kuma kuyi sauri ku karasa na ku 'yan rana su karɓa. Za'a dinga biyan kowacce dubu ashirin a wata." Tana gama fadan haka ta kalli masu bata abinci. "A kawo min kalaci na." Nan muka yi tsalle ni da Amira, saboda kwanan aikin ne daman muke gudu, ga kuma makudan kudin da muka ji ta ambata. Ni ko rabunsusu wallahi ban sa rai ba. Ina ta faman sauri babu ko waiwaye shiga wancan lungun, kurda wancan hanyar saboda muna da dan nisa da gidan sarki. Ban taba kawo wa raina abin hawa ba saboda rashin kudin biya. Da zafina na isa gida ina dokin yi wa Inna albishir. Tunda ga tsakar gida na fara jiwo nishinta da kakari alamar ciwanta ya tashi. Na wancakalar da takalman na karasa a guje tare da tallabo ta. A rude nake fadin, "Inna, ina kika ajiye inhaler?" Sai neman san karewa take ta faman yi. Na ga wawtata dana tsaya tambayarta, alhalin nadade da sanin cewa ta kare. Haba, a guje na fice gidan kamar mahaukaciya, nayi hayin kwalta kyamis din Dayyabu, sai zufa nakeyi na fada shagon ina ta haki, na ce: "Dayyabu ka dubi girman Allah, kaba ni bashin inhela, wallahi na sami aiki gidan sarki da an biyamu zan kawo maka kudinka, bazan sa'a ba insha Allah" kin tabbatar? Yafada yana gargadina da hannu. Na durkusa, wallahi Dayyabu zan kawo kaji na zantse "yadda ya miko min maganin nace na gode" sai na kwasa a guje. Da zuwa na isketa ta kai kasa warwas na shiga shaka mata ina dan fesawa cikin mintuna ukuzuwa hudu komai ya tsaya. Nayi ajiyar zuciya, Allah mai yadda yaso yanzu da aikin rana nake fa? Nadaga hannu sama nace, Allah na gode maka, Ubangiji ka kara rufa mana asiri. A hankali naji tace Ameen na kalleta nace sannu inna. Tace yauwa Ahankali, ya aka yi kika dawo da wuri haka? Na labarta mata yadda aka tsara sai na ga tana murmushi, ni kuma na mike zuwa tsakar gida na ga wacce dabara zan yi mana a matsayin abincin rana. Ina mamakin mutane, gabanka faram faram, amma bayan idonka arinka zaginka ana gulmarka. Su yanzu idan gimbiya tajisu yazasuyi ko basu tunanin cewa tunda naji zan iya kwarmata mata? Naci gaba da sauraransu "kinsan duk abin nan, wallahi ganin ita ce bababba kuma sarki duk yafi ji da ita, sannan kowa gidan tarairayarta yake yi ana lallashinta". Kware kuwa saboda ko wani abu ake son mai martaba yayi, idan ta kife ciki wallahi ba yayi sai da ra'ayinta. "mts! Ni ina ganin harda da rashin 'ya'ya dayawa ga sarkin, kinga fasu duka shiddane a gidan ita kadai ce wurin uwargida su ta sallah, kowa na da biyu biyu, sai Amarya da ke da daya namiji shi yasa duk suka tsane ta sai kace ba Allah ne ya bata ba" ke kuwa sun tabbatar ta haifo MAGAJI. Duk suka kyalkyale dariya harda tafawa. "Wai ni ya maganar auren gimbiya?" "Uhum! shu'umin mijin ne yaki zuwa har yau, kin san idan sarauta ta hadu da sarauta dole a baza MULKI. Amma naji an ce ya kusa zuwa nan gidan zai yi wata biyusannan iyayen su zo maganar sanya rana" wannan wace irin al'ada ce haka? "Ke ma kin gani, gidan nan ai sun yi bin da yafi haka kawai tsabar ISA ce". kinsan abinda yafi bani mamaki tace A'a". ,Wallahi kullum idan muna tare da gimbiya ita ce mai nemansa a waya, bai ta tafi bugo mata ba". suka kara dariya tace, "YARIMA!!! Wallahi yarima na wahalar da gimbiya, ina tunanin sarautarsu tafi wannan zafi". ko? Kware kuwa, ki ga fa mulki irin na gimbiya da giman kai, amma wallahi cikin kunnena naji tana kwantar da murya tana rokonsa kada ya ajiye mata waya". To ko bai sonta? Cikin sauri ta kai mata duka. "Yi shiru ban ce ba, domin ba a jimutuwar sarki a bakina ba". yaushe zai zo? "An ce talatar nan". kin san da maimartaba da babanshi wasu irin abokai ne na kud-da-kud, kara tu ma tare suka yi a kasar waje". , ke a Ina kika ji? ""ya za ki tambaye ni bayan kakar innarmu a nan ta yi aiki?" "Uhm lallai, tashi ki tayani kwaso wannan guga zan yi na zannuwan gado". Na biyu da kallo a kaikaice ina kara luliya hirarsu cikin kwakwalwata, kafin daga bisani na wancakalar da shi. Na dage cikin bada himma ina aiki na baji ba gani kamar daga sama naga Gimbiya da tawagarta sun zagaye ni. ' Yarbaba Wacce ke hannu damanta ta ce. " Allah ya ja da ran Gimbiya, shin ko wannan kike magana? " Kafin ta yi yunkurin magana tuni 'yan 'yan cikina sun kada, nan da nan gudawa ta kusa kubuce min cikin wando, tunani na ko laifi na yi. Ta kalle ni sama da kasa kafin tace, "a zo da ita daki". suka juya. ' Yarbaba ta daka mini tsawa. " Saki wannan aikin maza ki zo Kiran Gimbiya". kwalla suka cika min idona, muna tafe ina addu'ar Allah ya tserar da ni. Da shigarmu ta sallame kowa suka fice aka barni da ita. Ta kalle ni a yatsune, "Me ye sunanki? " Na ce, "Humaira". Ta rausayar da kai, "Na yaba da hankali, Nutsuwa da kuma kawaye ki. Kina da kyakkyawar tarbiyya kwarai da gaske, saboda haka na dauke ki a matsayin Wacce zata dinga kula da yarima idan yazo da safe kawai, cikin masu aikin rana ma zan sami guda domin ba zai so 'yan aikin dare ba sai dai wadanda ba a rasa ba. In son da safe da kika zo ki Kai masa ruwa a tasa cikin al'adar gidan nan take, zai wanke kafarsa kafin ya sakko daga gado ma'ana bayan sallar asuba. Ke ce Zaki dinga wanke masa kewaye da gyaran dakinsa tare da bashi kalaci, sa sauran kulawa har zuwa karfe biyurana, kafin ta ranar ta karba". Dadi ya kume ni na rusuna cikin girmamawa na ce. "Godiya nake Gimbiya". Ta kawar da kai, "Na sallame ki". Ta fada ba tare da ta kallo inda nake din ba. Na kara russunawa karo na biyutare da fadin, "Godiya nake Gimbiya". suna mike tsaye shima kafin na Kai ga tafiya sai da na dan rusuna mata alamar girmamawa. Sun nayi gaba abina. Washegari mun dukufa gyaran sashen da yarima zai sauka, an kawata wurin komai an saka sabo wai har da sutura aka saka zuba mishi cikin sif, shin dama tsinken raginsa zai zo? Kai! wannan al'ada da wannan mulki da tsauri suke. Shi mulki, ita mulki, na ga wannan so yayya. Gulmar mutanena ta kara katsen tunani da hasashen da nake yi. "Gimbiya na wahala da kowa a gidan nan". Inji Rabi Mamman. Ayyo ta amshe tana murmushi, "Baki ji abinda sarki ya fada wa matan gidan nan ba?" "Don yace ita ce sarautar sai a yi ta amfani da ra'ayinta, ga wuri a ce babu mai ra'ayin kansa sai abinda ta zartar?" "Mulki ke nan!" "Ni abinda ya fi damuna wallahi da aka bar mu a haraba na so ace muna 'yan ciki-yan ciki don mu ga kwakwaf! Duk fa sabbin daukar nan ne ta raba a nan din, ashe daman saboda zuwansa ya sanya aka karo BAYI, ana yi da kai ya fi ace ba a yi da kai". Ta yi dari, "wannan haka. sai mu jira jibin mu yi kallo, Allah ya taimake mu ya zo da irin na su bayin, watakila mu sami mazaje ciki ko kuwa?" "In sami miji dai malama ke Ina sama'ila Tasawan? " Ta buga tsaki, wannan fa mayaudarine ba aurena zai yi ba sai shegen wayo kalma idan an bamu albashi sai ya kalallame ni ya amshi rabi ko da dada, ba na fadawa. Kuma cikin matsala yake kin ji wayo, ko ke kin ga mijin aure a nan?" "Ina! Wallahi da sake ku yi mishi korar kare mai wayon tsiya". Ni dai a nan na barsu saboda na gama aikin na nan bangaren, na koma bangaren Gimbiya, sannan na karasa wanda na baro.
null
Idan kana duniya zaka ga abin mamaki kala-kala. Duk inda ka gitta kamshi ne, Gimbiya ta ci kwalliya ta kin karawa. Motocin ta ne a jere wanda ke dauke da sunanta, GIMBIYA daya GIMBIYA biyuhar zuwa GIMBIYA goma, rantsatsun motoci suke na zama ni, mu ne cikin sahun gaba zamu je taro Yarima, magana ba aiki ba, don haka na tsuke bakina, Ina kara mamakin wannan shagali. Lallai Gimbiya na matukar kaunar Yarima, hatta sarki da matansa ba su a bar su a baya ba, wajen tsara yadda za a tarbi wannan gagarumin baki. Inda za a hadu kamar yadda aka tsara nan, muka tarar da su, don haka ba tare da bata lokaci ba aka dungumo zuwa fadar Mai martaba don Kai gaisuwa. Mu kam tuni kowa ya kama tsagin da aka bashi don fara gudanar da aiki, ni kuwa inda Allah ya taimakeni a dai-dai wannan lokaci na gama a takaice 'yan rana, za su karba, don haka tuni na harhada yanawa-yanawa na yi gida kafin kuma gobe da safe. Yau ma labarin ya sha bambam da na klm, Inna ta dinga kyalkyala dariya, tana fadin, " labarin gidan sarki bai karewa Humaira, ni dai har na fara gajiya saboda tun da kika fara aikin nan, kuma da sabon labari ake zo mini, babu maimaitawa. Kinga ni na manta wallahi inhelar ta kusa karewa ki koma wurin Dayyabu ko Allah zai sanya ya kara baki wata kafin biyan ki" . Na ce, "to Inna, bari na yi sallar la'asar na je mu gani in zai bayar". Cikin yardar Ubangiji kuwa muka yi sa'a ya bayar, amma cikin kashedin lallai da an biyani na Kai masa kudinsa. Washegari na isa kan ka'ida kamar klum, sannan sashen Yarima na yiwa tsinke masu tsaron kofofin ko'ina, na wuce suna tsaye ana gudanar da aikin tsaron. Masu dafa abinci su dukufa. Na hanzarta zuwa falonshi na hau gyara ba tare da an sami wani kuskureba, sannan na shiga dakin kwananshi. Abinka da rashin sabo, sai kawai na tsinci kaina da faduwar gaba, nan take na karanto, 'Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un". Barci yake sosai, daga shi sai gajeren wanka, ya kure na'urar sanyaya daki (A/C), dakin yayi karara don tsabar sanyi. Na kalle shi sosai, jin dadi sabo duk wannan uban sanyin amma bai rufa ba, na yi saurin fadawa makewayin na ci gaba da wankewa, tunani ne ya tayar da shi, saboda lokacin da na gama na fito sai na tarar da shi zaune saman gadon. Da ma tuni na gama hada mishi ruwan wanka, da sassarfa na karaso wurinshi tare da durkusawa. "Barka da tashi Yarima, da fatan ka wayi gari cikin koshin lafiya" "Barka da tashi, mai ya kawo ki dakina da sassafe kin hanani baki?" "Na kara yi Kasa da kai. Allah ya huci zuciyar Yarima, tuba nake yi, wallahi ban zo dakinka don na takura maka ba..." "Ke!!" Ya daka ni tsawar da sai da hanjin cikina suka kada. "Ba ni amsar da na bukata." Ya fada cikin fada-fada kamar zai bugeni. Na yi sunkui da kai Ina fadin. "Ni ce mai kula da nan bangaren... Budewar kofar da aka yi ne ya sa nayi shiru. Gimbiya na gani cikin doguwar rigar irin ta baki mai Karamin hanu ya dalla mata wani rainannen kallo kafin ya ce da ita. "Yrnyr me zata yi mini?" Maimakon ta ba shi amsa, sai ta dubeni. Me ya rage? Gyaran gado da sharar nan." Na fada Ina nuna tsakar dakin, "sai kuma kawo karin kumallo." "Da kyau, je ki hado kalacin ki kawo mishi, idan yayi wannan a gyara dakin," inji ta. Na yi saurin cewa "an gama Gimbiya." Sannan na yi waje, ban sani yadda suka kare ba. Tafe nake, Ina al'ajabin wannan tsayayyen Yarima, shin ko gaskiyar 'yan gulma ne ba son Gimbiya yake yi ba? Idan kuwa haka ne lallai akwai matsala! Bisa kaina na doro tiren saboda ba ni iya dauka da hanu, akwai nauyi. Gimbiya ta tafi, amma shi yana inda ya ke, jallabiya kawai na gani ya saka. Na zuzzuba mishi komai, sannan na hada mishi ruwan shayi (tea) kafin na zuba sukari na dube shi kadan. "Wane adadi ne kake bukata?" "Au! Ni kike hadawa?" Tambah taso ta bani mamaki amma sai na sunkuyar da kai cikin girmamawa na ce. "Allah ya taimaka, duk kai nake hadawa karin kumallo." "To na koshi, dauke kayan ki, ba na ce, ki ce wa wacce ta aiko ki ba zan ci ba." A rasa ni na dago kai. "Allah ya taimakeka, ba gardama zan yi maka ba, sai dai Ina rokonka don Allah ka rufa mini asiri ka amshi kalacin nan, lallai rashin amsarsa na iya haifar min da barin aikina a gidan nan." "So what?" Ya fada yana yarfe hannaye. Idona ya cika da kwalla na yi Kasa da murya. "Don Allah yallabai ka yi hakuri kada ka yiwa kanka horon yunwa, ni matsalar Zata shafa." "Me Zata yi miki?" Ya tambaya ni. "Komai ma, ni dai kayi haka ko na yi maka lafiya?" Yanayin yadda na yi mishi tambaya yasa na ga kamar ya dan tausayamin, sai ya ce, "Ba ni na hada da kai na." Na yi saurin mika mishi kafin ya gama. Zaune nake har ya gama, sannan na kwashe kayan na fita. Lokacin da na dawo har ya shiga wurin, na yi hanzarin gyara gadon, sannan na share dakin. Na koma wajen na ba shi mintuna talatin, sannan na koma. Har ya gama shiryawa, na yi turawa! Jeans da T-shirt ya saka, maimakon alkibar da na ga Gimbiya ta kawo masa. Na durkusa a gabansa. "Allah ya taimaki Yarima, kake bukata?" "Ba tare da ya kalle ni ba," yace. "Ina bukatar a kyale ni na huta." Na dan sunkuya, "A yi huta." Sannan na juya na fita. A bakin kofa muka yi kicibus da Gimbiya, na kwashi gaisuwa kafin ta shiga. Tuni 'yan rakiya suka dunga a bakin kofa. Ina can ne zaune saman dakalin filawowi na hanga ta fito rai bace. Watakila wata maganar ta yi masa marar dadi. Zuwa cikin saurin, 'yan rakiya suka fara zubarwa filawowi irin yadda aka zubarwa Gimbiya masu kyau da kamshi. Ya tambayi su, "Kai mene ne haka?" Suka amsa, "Gimbiya ce ta aiko mu, wannan shine aikin mu." "Ku bace mini da gani, ba na so!" Tuni suka tsorata, "Don Allah yallabai ka yi haka, Gimbiya ba zata ji dadi ba, matukar muka je mata da wannan sakon." Ya nuna su da yatsa, ku bace min da gani tun kafin ran ku ya baci, na ce, "Bana so ku ce Gimbiyar na ce bana so!" Da sauri suka bar wajen. Ya nufi wurin jimina yana bata abinci a baki suna wasa. Sai fata rai a bace, ina dai hng su da juyo abinda suke fada. "Ka ce ba ka so abinda na sanya?" Ba tare da ya kalle ta ba yace. "Kwarai kuwa." "Sannu me?" "Ba na bukata." Ya bata amsa kai tsaye. "Wai Yarima mai yasa kake so bata mini rakiya?" Ya ci gaba da wasa da jimina kafin ya ce. "Kike batawa kanki dai, kinsan ni ko wane ne mu, tsarin mulkinmu ba haka yake ba." "Mts! Ta buga tsaki, fuuu! Ta yi cikin gida. Na yi kadake, Ina jimamin wannan al'amarin ko don yana ganin ya fata kyau shi yasa? Ni dai har lokacin ta yi bai koma daki ba, yana ga waccan tsuntsu bane ya ga waccan, na yi tfyt. Ranar da ta biyuna iso da karin gwiwar aikina, sannan na gama da falon, na shiga ciki. Sabanin jiya yau, idonsa biyuyana zaune a bakin gado, hannsa rike da waya. Na karasa da sauri don Kai gaisuwa, ya amsa fuskarsa babu yabo, babu fallasa. Na mike don zuwa kewaye na wanke ya dakatar da ni. "Zauna, me Zaki yi ne?" Na ce, "zan wani kewaye ne kafin na gama hada kalaci ka kimtsa, sannan na gyara nan din." "Barshi, bude durowar cikin ki fiddo duk kayan da ke ciki, ki Kai su falo ki zo ga jaka cikin ki jera mini wadanda ke ciki." Gabana ya yi mummunan faduwa, tsadaddun kayan da aka yi mishi oda daga kasar Ingila zai fitar? Lallai bai nemi zaman lafiya shi da Gimbiya ba, wane irin mutum ne shi mai wuyar hali haka? Aikin nake, amma Ina tunanin har na gama, na fara jera masa nashi. Ya mike tsaye ya ce, "Fiddo mini kala daya zan sanya kafin na fito." Koyan magana, na ce, "To." Na rasa, zan fidda masa duk ya daure ni, yadda na fahimce shi mutum ne, ba a yi masa gwaninta, salon wulakancinsa ya sha bambam da na Gimbiya. Na ci gaba da karanto addu'o'in samun sauki da kare fitina, domin Ina gujewa wulakancin mutane, musamman shi da na fahimci tsaye yake, ita kanta Gimbiyar shakkarsa ta ke yi. Wani farin boye ne mara nauyi, ma'abocin taushi da laushi na ware masa cike da fargabar kada ya ce ba ya so, ko ya gwasale ni. Da sauri na kammala shiri tare da ficewa dakin, bana son ya fito, Ina ciki haka Ina ganin bai dacewa ba ne. Idan ya gama kintsawa na dawo na gyara sauran wuraren da suka rage. Na fada kicin don hado abin kari, na tarar da su Rabi ita da Murja sun gama kammalawa suna zaune da Rabi'u mai tsaron kofa sai tattaba su yake yi, inda sabo na saba da ganin haka, tun muna bangaren Gimbiya shi yasa har yau na Kasa sakarwa su Rabin fuska, ballantana shi sai sun ji motsi kaga gudu, amma sun ga cewa ni ce za su dawo suci gaba. Ba ta su nake ba, sun san hakan. Na kwashi kayan na yi falo, na sami kujera na zauna don kara bashi lafiya. Ina yi Ina kallon agogo har kusan mintuna goma sha biyar sannan na mike dai-dai lokacin da ya turo kofa zai fito. Na yi saurin durkusa cikin girmamawa, na ce, "Kalacin ne zan kawo maka, wallahi tun da zuwa ya hadu lafiya na ne kusan mintuna goma sha biyarke nan Ina zaune don na bari ka kammala shiryawa, bayan ka fito, amma a gafarce ni." Shiru naji yayi, gashi kuma a tsaye. Na dago Kai na sai naga yana murmushi, ya tsuramin ido. Na yi saurin sunkuyar da kai cikin faduwar gaba Ina mamakin kayan da na fiddo masan, ne ya saka, ba tare da ya sauya. Muna haka, Gimbiya ta shigo, ta ci uban gayu sai kamshi ke tashi a jikinta. Ta dube shi, "Wannan kayan fa?" "Wannan na tarar a dirowa sun ciken guri, na ce a kwashe a fitar." Da sauri ta fita ba tare da ta yi magana ba. "Ke ba ni ruwan zafi na sha ki ji." Ya ce da ni. Yana cikin kalacin Dogarin sarki ya shigo Ina rakube, ina jiran, ya gama na kwashe kayan. Ya kwashi gaisuwa kafin ya ce, "Allah ya taimaki Yarima, sarki ne ya turo a yi kiranka da gaggawa." "Ina, kalaci da na karasa zan kawo kaina." Ba dogari ba, ni kaina sai da na Kai duba na ga Yariman. Hakan sa kwance yana kurbar shayi, na jinjina kai Ina addu'ar Allah ya tserar da mu wani mutum ya fi Gimbiya IZGILANCI!!! Dogari ya fita sukuku, ya gama shan shayin ya dubeni, na yi saurin kawar da fuska saboda shi din nake ta kallo tun dazun. Ganin haka yasa ya fada fadin abinda zai ce, ya mike kawai ya yi waje. Dama a ka'ida dk abinda Yarima ya ci idan ya rage ni zan juye na tafi da shi gida yau ma, kamar yadda na juya a lokacin da na juye uban farfesun kaji da soyayyen kwai da agada cikin kwanona na rufe, na koma dakinsa na gyara. Na bata lafiya sosai wajen gyara dakin, saboda har zanin gado na sauya. Na goge ko'ina bayan na gama shara, sannan na fasa abubuwan kamshi (fresheners). Dakin ya yi yadda nake sonsa sosai, sannan na fada bandaki na shige can kuryar inda ake wanka, na fara wankewa, sannan na fito. Yarima na gani tsaye ya gama fitsari, Allah ya taimake ni ya maida wandonsa yana kokarin fita, ne na fito, amma a alama bai san Ina ciki ba, na jage-jage da kumfa. Na tsorata kwarai da gaske, na zuba Kasa cikin kidima da furgici, kwalla na shatata a idona, kukan da mutum kan yi, lokacin da ya ga samu rashi kuma ya gitta. "Na tuba, na bi Allah, na bi ka Yarima. Ka taimake ni, ka yafe mini, kwarankwatsa dubu ban sani ka shigo ba, don Allah kayi mini rai ka yafe mini?" Abin mamaki sai naga yana murmushi tare da fadin. "Tashi tsaye, kewaye kike, mike babu komai ni ne zan baki hankali saboda lafiya na ne". Nan take na saki ajiyar zuciyar tare da goge kwallana na dan rusuna na ce, "Nagode kwarai, amma Ina rokonka da kar ka fadawa Gimbiya matukar ta ji karshen aiki na ya zo a gidan nan". Ya kara murmushi, ya ce, "kwantar da hankali na yi miki alkawarin babu wanda zai ji wannan magana". Yana fita na fadi Kasa dabas! Ina godewa Allah, ni dai Allah ya dorani saman Yarima, wasa-wasa yana daga mini sosai. Lokacin da na fito yana kwance saman gado, kaina Kasa na yi hanyar fita. Can Kasa naji muryarsa, ya fadin, "Idan ki huta ki kwaso kayan nan da kika fitar". Na rusuna ba tare da na dubi inda ya ke ba na ce, "To". Wane hutu gare ni lokacin da Yarima ya sanya ni aiki ko so yake yi, Gimbiya ta shigo ta rafshe ni? Tas! Na kwaso su, suka ce na jera su cikin jakar da ba kwashe kaya a ciki, Ina cikin yi Gimbiya ta shigo. Bakin gadon ta zauna cikin 'yar shagwaba naji tace masa, "Ba ka shiryaba?" "Ina zamu je?" Yayi maganar cikin halin ko'in ki "Haba Yarima tun jiya fa da marece na Snr da kai zamu je super market, kuma yanzu da muka fito fadar sarki na kara tuna maka". "Ki maida tufa zuwa gobe, yau na gaji da yawa". "Aikin me kike yi?" Ta bukata. Yace, "Noma". Ta ce, "Humaira taso ki fita". Na yi zubur daman jiran haka Yace ke zauna kici gaba da aikin dana sanya ki. Haba Yarima, me za ki yi idan muka gama ta dawo, ta karasa, saidai keki tafi idan ta gama kya dawo ki karasa, tunda maganar ta zamar miki dole. Ya dubeni cikin fada, yace nace kici gaba da aikin gabanki ko zata hanaki ne? Cikin tsananin fushi tabar dakin na juyo, Ina hawaye kamar famfo, na tabbata niya jawowa bala'in, sharben dana keyi yaji amma baice komai ba sai tsaki da yake ta famanyi. Na mike zan fita, yace zo nan, na dawo na durkusa, har sannan hawayen basu daina zuba ba, me akayi miki? Tambaya tashi ba maraba da rainin hankali, bakiji ni bane kikai shiru? Na bude baki a hankali, na ce bakomi, shagwaba ce? Ya tambaya, wa zanyi wa? Na tambayi kaina, kina jina na girgiza kaina, dakin san yanda kuka yake maidaki da baki dinga yi ba, tashi ki tafi. Maganar sa ta tsaya min a rai matuka. Karfe biyuna isa gida na tadda inna tayi mana danwake nayi sallama na karasa bakin murhun, sannu da aiki inna, yauwa sannu Humaira ya aiki.... Maganar ta sarke mata yayin data kalleni cikin kulawa, ya naga kamar kinyi kuka? Hawaye suka zubo min kafin na fara bata labarin abinda ya faru, na jinjina kai cikin tausayawa, kuma komai zakiyi kisa a ranki yana ganinki. nna bazaki gane ba... Iyakar ganewar kenan tunda na ambaci Allah kuma komai a duniya idan akace Allah an gama saimu bar lamarin a hannunsa, nayi shiru, tace dauko kwano na zuba miki danwaken da zafinsa nasan kinason me zafi. Nadan bata fuska cikin nuna damuwa nace wllh, inna kinason wahalar da kanki yau ma kiga uban abincin danazo dashi, ina maganar, ina bude kwanon da ledar dankalin yau, naman ma yafi na kullum yawa. Tace nasan haka, nima kwadayin danwaken yasani yinsa. Inna banason kina wahala, kinga hayakin nan matsalane ga lafiya batace komi ba, har muka gamacin danwaken, nace yau kam inna gaskiya bazanje Islamiyya ba kaina ke ciwo. Sumayya tace yaya malam, yace mu fada miki wannan watan ma an yafe mana kudin wata, nayi murmushi Allah ya saka da alhairi, inna tace ameen. Da safe kamar kyllum na gama bayan na gama duk aikina yauma idonsa biyu amma ya barbaza takardu akan gado yana rubuce-rubuce akai. Na gaisheshi ya amsa min a takaice saboda aikin yasha kansa. Harna kammala komai yana nan, sannan na fita na kawo masa kalaci, lokacin yana kwashi takardun na ajiye cikin girmamawa, sannan na koma gefe. Ina jira ya na kwashe. "Kinga nifa nayi wanka, ina jiranki ne, kizo ki bani kayan da zan saka," gabana ya fadi. Nayi saurin tashi, ina bashi hakuri na nufi gurin kayan, to meyasa Gimbiya bata fada min wannan ba ko mantawa tayi saboda ban taba sanin har kaya ni zan zaba masa ba, na dade tsaye, sai nayi la'akari da ranar na zabo masa jeans brown kolo da shirt cream kolo mai ratsin layin red nd blue na ajiye akan gado, ina karanto Innalillahi... a zuciyata. Abin mmki har ferfesun kan ragon yasha kai gaskiya yau yaci abinci sosai kwai da plantain ne kawai bai ci ba. Na kwashe kayan nakai kicin, na ajiye sannan naje store na samo ledoji, ina cikin juyewa kawai, nagama mutum a tsaye akaina ya kura min ido, nayi saurin durkusawa nace ko yana bukatar wani abu? Ya girgiza kai, naci gaba da juye abincin na ajiye bread daban, ya wuce abinsa, nagama na koma dakin na gyara wajen daya, bata na ninke kayan daya cire na zubasu a kayan wanki. Falo ya dawo ya zauna, bai tabayi ba, kenan anan gimbiyar ta tarar dashi yau kam yana arzikin suna kansa, tunda fitowa biyusai naga suna dariya... Ganin haka yasa ya fada fadin abinda zai ce, ya mike kawai ya yi waje. Daman a ka'ida, abinda Yarima ya ci idan ya rage ni zan juye na tafi da shi gida yau ma, kamar jiya na juye uban farfesun kaji da soyayyen kwai da agada, cikin kwanona na rufe sannu na rufe sannu na koma dakinsa na gyara. Na bata lafiya sosai wajen gyara dakin, saboda har zanin gado na sauya. Na goge ko'ina bayan na gama shara, sannan na fesa abubuwan kamshi (freshners). Dakin ya yi yadda nake sonsa sosai, sannan na fada bandaki na shige can kuryar inda ake wanka, na fara wankewa, sai da yayi kal snn na fito. Yarima na gani tsaye ya gama fitsari, Allah ya taimake ni ya maida wandonsa yana kokarin fita ne na fito, shima da alama bai san Ina ciki ba, hnn na jage-jage da kumfa. Na tsorata kwarai da gaske, na zuba Kasa cikin kidima da furgici, kwalla na shatata a idona, kukan da mutum kan yi a lokacin da ya ga samu rashi kuma ya gitta. "Na tuba na bi Allah na bi ka Yarima. ka taimakeni ka yafe mini, kwarankwatsa dubu ban San ka shigo ba, don Allah kayi mini rai ka yafe mini?" Abin mamaki sai naga yana murmushi tare da fadin. "Tashi tsaye, kewaye kike, mike babu komai ni ne zan baki haka saboda laifi na ne." Nan take na saki ajiyar zuciya tare da goge kwallana na dan rusuna na ce "Nagode kwarai, amma Ina rokonka da kar ka fadawa Gimbiya matukar ta ji karshen aiki na ya zo a gidan nan". Ya kara murmushi, ya ce, "Kwantar da hankali na yi miki alkawarin babu wani abu zai ji wannan maganar." Yana fita na fadi Kasa dabasu! Ina godewa Allah, ni dai Allah ya dorani saman Yarima wasa-wasa yana daga mini sosai. Lafiya da na fito yana kwance saman gado, kaina Kasa na yi hanyar fita. Can Kasa naji muryarsa yana fadin. "Idan kin huta ki kwaso kayan nan da kika fitar". Na rusuna ba tare da na dubi inda ya ke ba na ce, "To". Wane hutu gare ni da Yarima ya sanya ni aiki ko so yake yi Gimbiya ta shigo ta rafshe ni? Tas! Na kwaso su yace na jera su cikin jakar da ba kwashe kaya a ciki, ina cikin yin Gimbiya ta shigo. Bakin gadon ta zauna cikin 'yar shagwaba naji tace masa, "Ba ka shiryaba?" "Ina zamu je?" Yayi maganar cikin halin ku "Haba Yarima tun jiya fa da marece na San da kai zamu je supermarket, kuma yanzu ma da muka fito fadar sarki na kara tuna maka." "Ki maida tufa zuwa gobe, yau na gaji da yawa". "Aikin me kayi?" Ta bukata. Yace, "Noma". Ta ce, "Humaira taso ki fita". Na yi zubur daman jiran haka Yace ke zauna kici gaba da aikin dana sanya ki. Haba Yarima magana fa mukeyi idan muka gama ta dawo ta karasa, saidai keki tafi idan ta gama kya dawo ki karasa tunda maganar ta zamar miki dole. Ya dubeni cikin fada yace nace kici gaba da aikin gabanki ko zata hanaki ne? Cikin tsananin fushi tabar dakin na juyo ina hawaye kamar famfo, na tabbata niya jawowa bala'i, sharben dana keyi yaji amma baice komai ba sai tsaki da yake ta famanyi. Na fita na durkusa har sannan hawayen basu daina zuba ba, me akayi miki? Tambayar tashi ba maraba da rainin hankali, bakiji ni bane kike shiru? Na bude baki a hankali na ce, bakomi, shagwaba ce? Ya tambaya, wa zanyi wa? Na tambayi kaina, kina jin hawaye kaina, dakin san yanda kuka yake maidaki da baki dinga yi ba, tashi ki tafi. Maganar ta tsaya min a rai matuka. Karfe biyu na tadda gida na tashi mana danwake nayi sallama na karasa bakin murhun, sannu da aiki Inna, yauwa sannu Humaira ya aikin.... Maganar ta sarke mata yayin data kalleni cikin kulawa, ya naga kamar kinyi kuka? Hawaye suka zuba min kafin na fara bata labarin abinda ya faru ta jinjina kai cikin tausayawa, kiyi hakuri Humaira Allah yana tare dake kedai ki sanya tsoronsa a cikin zuciyarki kuma komai zakiyi kisa a ranki yana ganinki. "Tace nasan haka nima kwadayin danwaken yasan yinsa. Inna banason kina wahala, hayakin nan matsalane ga Alfari bata ce komi ba, har muka gamacin danwaken. Nace yau kam Inna, gaskiya bazanje Islamiyya ba, kaina ke ciwo. Sumayya tace yaya malam, yace mu fada miki wannan watan ma an yafe mana kudin wata. Nayi murmushi Allah ya saka da alheri. Inna tace ameen. Da safe kamar kilumi nagama bayan nagama, duk aikina yauma idonsa biyu amma ya barbaza takardu akan gado yana rubuce-rubuce akai. Na gaisheshi ya amsa min a takaice, aikin yasha kansa. Harna kammala komai yana nan, sannan na fita na kawo masa kalaci lokacin yana kwashi takardun na ajiye cikin girmamawa, sannan na koma gefe ina jira ya karasa na kwashe. Kinga nifa nayi wanka, ina jiranki ne kizo ki bani kayan da zan saka, gabana ya fadi nayi saurin tashi ina bashi hakuri na nufi gurin kayan, to meyasa gimbiya bata fada min wannan ba ko mantawa tayi ba, ban taba sanin har kaya ni zan zaba masa ba na dade tsaye. Sai nayi la'akari da ranar na zabo masa jeans brown kolo da shirt cream kolo mai ratsin layin red nd blue na ajiye akan gado, ina karanto 'Innalillahi'... a zuciyata. Abin mamaki har ferfesun kan ragon yasha kai gaskiya, yau yaci abinci sosai kwai da plantain ne kawai bai ci ba. Na kwashe kayan nakai kicin na ajiye, sannan naje store na samo ledoji, ina cikin juyewa kawai, naga mutum a tsaye akai ya kura min ido. Nayi saurin durkusawa nace ko yana bukatar wani abu? Ya girgiza kai naci gaba da juye abincin na ajiye bread daban, ya wuce abinsa, nagama na koma dakin na gyara wajen daya bata na ninke kayan daya cire na zubasu a kayan wanki. Falo ya dawo ya zauna, ba tabayi kenan. Anan gimbiyar ta tarar dashi yau, kam yanzu suna dariya. Nansu ka kusa yini don ni har lokacin tafiya. Anan na barsu na harhada kayana, nayiwa su Rabi sallama na tafi. Misalin karfe shida saura kwata na dawo Islamiyya, natarar ciwon Inna ya tashi. Abun yau yafi na kullum, hankalina ya tashi na rude na shiga neman maganinsa bangani, kusan 7* ina tambayarta amsa ta gagara, duk inda nake zato na duba bangani ba. Na dinga kuka nan da nan na fyalla shagon dayyabu na fada shagon kamr mahaukaciya, ina fadin dayyabu ka taimakeni don girman Allah, ciwon Inna ya tashi, ka bani inhealer, wllh an kusa biyanmu a gidan sarki, kasa a lissafi... Ke fitar min a shago, bazan bayar ba... Na rushe da sabon kuka, na durkusa ina rokonsa amma ko a jikinsa naga cewar babu Sarki, sai Allah (dama shi kadai ne Sarkin). Sai kawai nabi hanyar gidan a guje watakila su Aisha sun dawo sun san inda ta aje adaidai kwanar lungunmu, wata rantsatstsiyar mota tasha gabana neman yanda zanyi ta kaina nake bata ita nake ba
null
Abun mamaki, sai naga Humaira ta fito daga gabar motar, ta taho ta rikeni. Humaira, lafiya, kika gigice kamar mahaukaciya? Nace wllh, Amira, ciwon Inna ne, ya tashi, narasa maganinsa, SubhanAllah, dama tare muke da yarima, gashi can a mota yace na rakoshi (chai! Diaris God ooo! Har anzo gurin?). Nayi saurin fiddo da idanu yarima? Lafiya? Meya kawoshi gidanmu? Tace, kinga yanzu ba wannan tym din, tambayoyin ta karasa mota cikin sassarfa. Da sauri naga ya fito, zo nan! Ya kirani da sauri naje shiga mota! Kamar jiran jira yake, ya fizgi motar da gudu ya nufi wani katon shagon magani, ya shiga gudu ya siyo magunguna, ya kara fitowa da gudu, ya kuma fizgar motar har gidanmu na fito guje, ya bani inhealer daya. Na shaka mata na kara shaka mata, ta riga ta gama galabaita cikin yana farko ne dan ishirinseconds ta sami kanta. Nayi ajiyar xuciya, sai sanann na farga da yarima dake tsaye na janyo jakar kayana yana kallo na fiddo zaniin shiga taro na shimfida masa akan kujerar katakon na umarce shi da ya zauna. Sai kawai ya yane zanin ya mikomi tare da zama akan katakon na sunkuyar da kaina. Ya kalli inna cikin girmamawa, yace sannu ya jikin? Tace da sauki yace, Allah ya sawwake, ya miko ledar. Yace magungunan nan, danAllah, a daina bari suna karewa. Nace, inna yarima ne, fa mijin gimbiya ta kara kallonsa. Mungode, fa mungode. Yace bakomi, inna, zan koma Allah ya kara sauki. Tace ameen. Nida Ameera muka rufa masa baya har bakin mota, na durkusa har kasa. Nace masa, nagode da taimakon da kayi min Allah, ya saka da alheri. Ya biya da gidan aljannah. Nima nace ameen. Yace amin, Allah ya bata alheri. Amira tace, Allah ya taimaki yarima, ni daganna, zan karasa gida. Na tayi ajiyar zuciya na dubi amira, nace, yarima, yazo gidanmu kuma ya akai, yasan unguwarmu daya? Ta kalleni sosai, tace muna tsaye ni. Rawila, muna ban ruwa in gaya miki. Ya fito a hanzarce, sai naji yana cewa, wasila ke xonan ina wannan yarnyr da take gyara min sashena? Tace wa yallabai? Yace, yar farar marar jiki, zaki ganta magana ma, bata dameta ba. Ya daka mata tsawa, ke yar doguwar nan nake nufi wace bata fiddo gashinta waje. Nan da nan na gane ke yake nufi na rugo. Nace, ko humaira kake nufi? Yallabai, zaka ganta kullum tana nade da carbi a hannunta? Yayi saurin cewa, kwarai ita ce kirawo min ita yanzu tana ina? Ya karasa maganar, yana dube-dube. Nace, tana gida, dama aikin safe takeyi. Yace, kinsan gidan? Tambayr ta bani mmki amma nace eh. Yace muje ki rakani, wllh, gimbiya ba tsan ya fito, kuma kinga da kanshi ya tuko motar. Na dubi amira, nace ko lafiya yazo nemana, amma wata kila, wani abun yake nema, bai gani ba. Wllh, bashi bane, na fahimci sonki yake baki lura da kallon da yake miki a dakin inna ba. Na kyalkyale da dry amira baki da sauki, kawai na fahimci, yarima mutum ne me tausayi kawai yana tausayawa rayuwarmu ne. Yanzu ko daura min shi akayi amira, ina zan kai yarima? Zata kara mgn na daga mata hannu kibar maganar nan, kin jahilci yarima ba haka yake ba. A dole tayi shiru. Bayan na rakata na isa gida na tadda inna harta tashi, tace "Yo ke ashe wannan maganin, ba irin wanda nake sha ba ne." Na amsa, na duba sainaga babban ne me tsada ya siyo a kwalinsa me 24, kuma da gani zai dade, bai kare ba. Yafi wancan girma da karfi nayi murmushi. Nace, ai wllh, mungode. Ina kuka hadu ne? Nace, wllh, inna, Allah ne ya kawo yarima na bata labari kamr yanda mukayi da amira, har yanda mukayi da dayyabu. Ta girgiza kai kawai, tayi ajiyar zuciya hrt har biyu kafin tace, "Allah kenan, buwayi gagara misali. Don Allah, gobe ki kara yi masa godiya." Nace, wann ai dole ne, inna Sumayya da Aisha sunyi tsuru-tsuru sun kasa cewa komai na wasan. Da wuri muka kwanta bacci yau a gidan Gimbiya, ta kwala min kira, na juya da sauri, ina mmkin wann sammako tare da adduar Allah, ysa bata ji labarin zuwan yarima gidanmu ba. Ta mikomin doguwar takarda, kibawa yarima idan kin shiga na karba, nayi wata irin ajiyar hrt. Harna gama komai bai tashi ba, na kawo kalaci, na zauna ina jiran tashin shi. Tunani kawai nake in banda rashi da talauci. Wannan aikin bai dace da yar musulmi, katon namiji yana kwance a gado ni, ina dakin, kuma ba muharramina ba. Na daga hannu, ya Allah, ka karemu daga sharrin shaidan. Na mikeni, na dauko masa kayn da zai sa na aje a gadon. Sai goma sha biyu da talatin ya fito, ina zaune a gefen kujera daga kasa, yazo ya zauna a kujerar dake fuskantata. Nayi zaman yan makaranta na gaidashi, ya amsa, ya tambayi jikin inna da sauki. Na fada ina murmushi, na sake satar kallonsa, nace, "Gaskiya, naji dadin hallacin dakai." Min jiya bazan taba mantawa ba. Inna tace a kara maka godiya, ya kalleni, yace, "Ba wani abu, kije ki kawo kayan kalaci." Harna, kai bakin kofa, yace, "Waya, baki takarda ki kawo min?" Nace, gimbiya ce, ita gimbiyar. Tace ki ajemin takarda, ki bani a hannuna? Da sauri na zube, cikin kidima, na rantse da wanda raina ke hannunsa, babu ruwanta, naga cewar, kana bacci kuma. To ki dauki takardar, ki mayar mata yanda ta baki na kalleshi, idanu jajur kayi hakuri, laifinane. Humaira, kinada matsala, wllh, abu kankani. Saiki tada hnklinki, musulmi aka ambaci, gimbiya a ciki, ba aikoki tayi ba? Na daga masa kai to ni kuma na aikeki. Na mike kamr wacce kwai ya fashewa a ciki, tana falo, ta kalleni cikin kulawa. Lafiya dai ko? Na durkusa, na mika mata, nace, yarima, yace, na kawo miki ta. Amsa ta bude, sai naga, tana murmushi, kice masa nagode. Na juya cikin kwarin guiwa, naje na gaya masa, harna fito, yace, "Humaira, zo nan." Ya nuna mini wuri, na durkusa, na sunkui da kai, ina sauraronsa jiya, inaso na tambayeki, na mance, ina babanku? Ya rasu! Yafi 6 minutes baiko motsa ba, dama inna ita kadai ce? Nace amsa masa uhm ita kadai ce, yayyenki nawa? Nace nice babba, wadannan yanmatan kannenki ne? Nace eh, sunawa ne? Su biyun daka gani, skul fa? Na daina zuwa amma su zasu koma wann hutun idan an koma, kefa? Nayi shiru, kinji? Baki magana ne? Nakasa cewa uffan wallahi saina sami bakina da yin nauyi, tashi ki tafi to tunda na bata miki rai kiyi hakuri (wai shema tana kallon daukaka) tsoro ya kamani ni wacece da yarima zai bata wa rai har ya bani hakuri, wann abu kamar asiri nakasa cewa kala, ya dan sassauta murya yanzu ya kikeson ayi kinki magana nace ki tafi kinyi jugum? Magana tana miki wuya ko? Na girgiza kai yayi murmushi yace to tashi ki tafi na mike na nufi kicin na fice ta kofar baya na tarar da mutanen ana sana'ar ko kallonsu banyi ba nace Allah ya ganar daku, wata irin yunwa nakeji na debo kalaci cikin wanda ya rage a bakar leda dankaline da kwai na tafi can baya na zauna inaci kamar daga sama na ganshi wani irin kallo yake min na tausayawa yace donAllah zauna kici kalacin ki na zauna amma na kasa cigaba da ci, a gaskiya baki kyauta ba dama baki kalaci ba ki hau aiki tun safe sai yanzu kusan karfe daya da kwata? Ya karasa zancen yana duba agogonsa, Nayi dan murmushi wallahi na karya tun a gida yanzu ne dai na dan jin yunwa, bai kara magana ba ya wuce abinsa. Suna zaune shi da gimbiya a saman wasu kujeru na fito da shirina cikin wata kokakkiyar atamfata kafata sanye cikin kodadden silifas da hijabina har kasa na wuce su ina ga yau ce rana ta farko dana taba tafia gida ya bini da kallo harna tsargu, gimbiya ta ware murya ta kirani na taho da sauri na zube gabansu tace yarima yace ku ba'a koya muku bankwana bane? Kafin nayi magana gimbiya ta surfan zagi dama bakice masa zaki tafi ba ko yana bukatar wani abu? Jikina ya dauki rawa yace tayi min bankwana dazu yanzu ne dai batayi min ba (Allah Sarki yarima bai san za'a zageta ba) kana bukatar wani abu ne da zata yi maka? Yace a'a to meye nayi mana wani bankwana keyi tafiyarki, sai naji yana dariya nidai har tuntube nakeyi don sauri. Ina isa natarar da inna sun shirya cikin kayan da basu da wata nagarta tausayin kanmu ya kamani nace sai ina kuma inna? Tayi murmushi tace ai nayi babban kuskure na manta yau ne ake bikin Harira yar gidan babanku Auwalu. Raina ya baci amma na kasa nunawa sai nace shine zaku tafi yau baku hakurin gobe? Ta dan harareni suwaye masu aikin abincin idan ba muba? Nace kai inna har yaushe zaki dinga wahalar da kanki akan wanann mutanen da basu san ciwonki ba cinmu da shanmu da suturarmu da uwa uba karatunmu? "Ai ba ɓangaran dahuwar zan tsaya ba, kinga akwai gyaran kayan miya, yankan albasa, alayahu, fere kabeewa da sauransu," na taɓe baki kawai na sauya maganar da cewa, "cikin satin nan naji ana cewa za'a biya mu saboda haka gaskiya inna har dunkuna sai munyi." Kuruci dangin hauka, in ba Humaira ba yaushe ana ta ciki za aita tsumma? Allah dai yakawo albashin lafiya, biyan bashi dai shine farko idan Allah yaso. Nace, "Amin." Na fiddo abincin da nazo dashi, suka ci suka yi kat, sannan ta mike, "kiyi kokari ki lega gurin 'yanmatan kafin lokacin islamiyyar." Da kai kawai na amsa mata. Ta yi murmushi, "maganar ku, a ta kulle?" Na dai yi shiru. "Don Allah kada kije kiyi wannan miskilancin cikin jama'a, ki saki jiki wani abu daurewa ake yi." Na dai yi murmushi kawai ta fita tana fadin, "Hali zanan dutse." Na dan watsa ruwa sannan na fiddo wata riga da siket a sosassen leshi wanda akalla zai yi shekaru 4, yana daya daga cikin na ganin sarki wanda nake takama da shi. Na yayyyafa masa ruwa tare da bigewa saboda cikwikwiyewar ta tashi. Farin gyale ya tashi saboda tsufa na yafa, sannan nasaka takalmin robata na zuwa biki, ko suna ruwan hoda. Na fito tare da jawo kofar gidan nadan sanya tsinken kara da dan icce gurin hancin na kulle kamar yadda muke idan zamu fita tare da kudurtar insha Allah da an biya mu kudi zan sawo mana kwado. Tafe nake kaina a kasa na wuce gungun samari kusan biyar, kwanar karshe da zan bita kai ni kofar gidan nayi karo da wata majalisar. Na dan gifta kadan na ji wani yace, "Kai yarinya har yarinya amma ba galihu." Karaf naji wani ya amshe, "Irinsu kuma sai shegen girman kai na banza, waccan yarinyar ita ake yiwa kirari da danwake kafi ubanka, a unguwarsu gidansu na dan nesa da na su Ibrahim Balarabe, an ce girman kan tsiya gareta saboda..." Maganar tayimin nisa, ban karasa jinta ba na shige gidan kawai. Inda sabo na saba da irin wadannan maganganun bakin samari, shi yasa bana mai da kai. Dalili kuwa shine ina yawan yin samari da farko, amma duk wanda zai zo sai ya yi amfani da talaucinmu ya nemi yi mini maganar banza, korar karen da nakeyi musu ne yasa suke yi mini shaidar mai kashin tsiya, kuma girman kan tsiya gareni, sannan danwake ce ni. Na kan yi mamaki, talauci hauka ne? Ina ganin tsira da mutumcin 'ya mace shi ne babban arzikin duniya da lahira. A nawa fa tunanin. Kamar duk lokacin da hidima ta tashi a kullum muna rakuɓe gefe, haka ma wannan lokacin. Zaune nake kusa wasu tsofaffin maroka ina kallon kowa yadda ake shagali bare wanda bai hada komai dasu ba, ya fi ni sakewa da gata saboda babu. Babu wacce ba ta ganni ba, amma ko kallon arziki har aka kira la'asar ko ruwa na shiga nace, "Yaya Harira sai Allah ya kaimu." Tayi watsi kamar ba taji ba, na kara maimaitawa, ta daka mini tsawa, "Naji." Na juya cikin abokanta naji wata ta ce "Kin sallame su?" Ta ce, "Wa?" Ta nuna ni da yatsa, "Ba 'yar marokan can ba ce?" Na dan juyo dan kallon wacce ta yi maganar. Ta yatsina fuska, "Wai 'yar uwarmu ce." Dayar na zaune da waya a hannunta tana latsawa tun shigowata ta kyalkyace da dariya, tare da fadin, "Shegiya Harira, wato wai ma ne?" Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki shewarsu, ni dai na yi waje ina mai takaicin irin wannan salon wulakancin, a ce duk sabga da salon irin wanda za a yi mana? Dama waccan karon an kira inna da 'yar aikin gida. A tunanina zan tarar da su inna su ma sun dawo saboda zuwansu Aisha islamiyya, sai na ga cewa ba su dawo ba. Na ɗauki littattafaina da hijabi bayan na gama sallah na fito... Shekara biyuda suka wuce nayi saukar Alkur'ani, yanxu ta biyuzanyi, wacce nake hadda, ga shi na gama littattafai da dama kamar su; ZADUl MUSLIM, HAKKUL MUBIN, KHAMSUNA HADITH, HUSNUL MUSLIM, BULUGUL MARAM... kai za su kai goma sha biyu yanzu wasu sabbi muka shiga irin su, ma'anar addu'a da fassarorinta, tarihin Annabawa da kissoshinsu, da sauransu. Acan na tarar da su Sumayya suka ce daga gidan bikin suka taho, inna sai anjima na kada kai kawai cikin raina nace ba ta gama bautar ba ko? A gida muka tarar da ita bayan mun tashi da nairarmu 300, wacce aka bada sadaka wani bawan Allah ne ya kawo. Tun a hanya na siyo mana taliyar leda daya, naira dari da goma, magi 20, gishirin goma sai mai na ishirinkwanti. Na san muna da ɗan sauran busasshen tattasai muka rago dari da hamsin, su Aisha sai tsalle ake yi gobe za a yi kalacin koko har da kosai. Ba ƙaramin dadi wannan labari ya yiwa inna ba, na ba Aisha ta siyo mini icce na ishirinashanar biyar. Nan da nan na dora dafadukar taliya. Saboda rashin kamawar iccen ya sanya ana kiran isha'i na sauke. Bayan munyi sallah na zuzzubawa kowa na gyara wurin na kauda duk kayan da na yi amfani da su, sannan ni ma na karasa saman tabarma nan waje farin wata ya haske ko'ina. Lomar farko almajiri yayi sallama da robarsa a hannu nayi saurin hadewa da hanzari don samun damar amsa masa sallamar. "Ance ana magana da Humaira." Wani gululu ya taso mini, dama na hango tsayuwar mutum jikin katangarmu tunda karamace, nasan cikin 'yan iskan samarin nan ne saboda yau na wuce majalisa da yawa, shi yasa ban cikin son zuwa gidan baba Auwalu ba, unguwar da hanyarta kamar nan aka tara samarin KANO! Ko motsi nakasa yi har yaron ya fita da amsar inna, wato, tana zuwa. Na fi minti biyar.a haka cikin nuna fushi inna tace, "Baki da halin zuwa kika sa nayi karya?" Raina ya kara ɓaci, wani abu sai iyaye, shin inna ta manta da cewar abinci nake ci? Ko kuwa nice na ce ta ba da amsa? "Sai kin gama shawara zaki tashi?" Ta katse ni tana fada. Na mike kawai ba tare da nace komai ba. "Wannan miskilancin? Wannan miskilancin?? Allah ya rabaki da shi Humaira, ace duk aikin duniya babu mai miki wuya sai MAGANA?" Na dan yi murmushi lokacin da na sako hijabi, maganar taso bani dariya, Inna kenan. Na fada a raina. Wani kamshi ya doki hancina, kamshi mai kwantar da zuciya da tarwatsa tunani zuwa wuri guda. Tsaye yake ya jingina da katangar, hannunsa goye a kirji. Na kasa kallon fuskarsa, na dan jingina ni ma dan nesa da shi kadan muna fuskantar juna. Ya yi magana shiru! Har kusan minti ishirin da biyar a kiyasin. Tun ina daurewa har tsayuwar ta fara gundurata, kuma da alama ni kadai yake kallo. Gaba da gabanta, na fada a zuci, inna da mutanen gari na kirana miskila, yau ga wanda ya shafeni. A tunanina shi yazo ba tare da na gayyatoshi ba. Wasa sabon aji har ana neman kusan minti arba'in haushi ya turnikeni, wannan wulakanci da yawa yake, amma zan ba shi minti ishirinnan gaba, matukar bai yi magana ba to zan yi tafiya. "Kai zo nan," tattausar muryarsa ta katseni lokacin da ya kira wani almajiri. Tsoro, fargaba da kuma razana duk a cikin wadannan 'yan sakanni suka shige ni, na dago kai tare da kallonsa. Tuni ya maida kallonsa ga yaron, har ya karaso.
README.md exists but content is empty.
Downloads last month
39